Wasan Tennis

Andy Murray ya lashe kofin Wimbledon

Dan wasan Tennis din Birtaniya, Andy Murray
Dan wasan Tennis din Birtaniya, Andy Murray

Dan wasan Tennis din kasar Birtaniya Andy Murray ya lashe kofin gasar Wimbledon a wasan karshe da aka buga a jiya, wato bayan ya doke dan wasan Tennis na daya a duniya Novak Djokovic da ci 6-4,7-5, 6-4.

Talla

Murray a yanzu haka ya kasance dan wasan tennis na farko dan kasar Birtaniya da ya lashe kofin gasar ta Wimbledon tun bayan dan wasa Fred Perry wanda ya taba lashe kofin a shekarar 1936.

Hakn na nufin Birtaniyan wacce ke daukar bakuncin wasan ta yi farautar wannan kofin na tsawon shekaru 77.

Wannan nasara har ila yau da Murray dan shekaru 26 ya samu ta kasance nasarar shi ta biyu inda ya lashe babban kofi a fagen gasar Tennis na duniya na Grand Slam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.