Kasuwar 'Yan wasa

Chelsea na farautar Rooney da Suarez

Dan wasan gaban Manchester United, Wayne Rooney
Dan wasan gaban Manchester United, Wayne Rooney Shaun Botterill/Getty Images

David Moyes yace Rooney ba na sayarwa ba ne amma Jaridun Birtaniya sun ruwaito cewa akwai kungiyoyi da ke farautar Rooney da suka hada da Chelsea da Barcelona bayan Dan wasan ya nuna bukatar ficewa Old Trafford.

Talla

A ranar farko da David Moyes ke zantawa da manema labarai a matsayin kocin Manchester, Kocin ya jaddada cewa Rooney ba na sayar wa ba ne, amma jaridar Daily Mail a Bitaniya tace Chelsea tana ci gaba da farutar dan wasan.

A cewar Jaridar, kungiyar Chelsea ta yi tayin linkawa Rooney albashinsa a yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar ke neman kulla wa da Dan wasan na kudi da suka kai Fam Miliyan 60, idan har zai nemi hanyoyin da zai fice Old Traffrod.

Luiz Suarez na Liverpool, yana cikin ‘Yan wasan da Mourinho ke farauta.

Jaridar Daily Mirror tace Mourinho zai tsorata Arsenal da kudi Fam Miliyan 40 domin mallakar Suarez bayan Arsenal ta taya dan wasan akan kudi Fam Milian 30.

Amma Liverpool ta jajirce dan wasanta ba na sayarwa ba ne.

Akwai kuma dan wasan Aston Villa Christian Benteke da Chelsea da Tottenham suka wa ransu.

Kungiyoyin biyu sun canza ra’ayi ne bayan ‘Yan wasan da suke farauta sun kubuce masu, inda Edinson Cavani ya kubuce wa Chelsea zuwa Paris Saint-Germain, Kamar yadda Davd Villa ya kubucewa Tottenham ya koma Atletico Madrid.

Jaridar Daily Star tace idan Har Chelsea ta kwace dan wasan Aston Villa, Tottenham za ta koma farautar Roberto Soldado na Valencia.

A wani labarin kuma, sabon kocin Real Madrid ya rufewa Manchester City kudirinta na bukatar Pepe, inda Carlo Ancelotti ya shaidawa Manuel Pellegrini cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.