Premier League

Rooney ya shiga damuwa a Manchester

Dan wasan Manchester Wayne Rooney a lokacin da ya ke sauka da jirgi domin wasan sada zumunci tsakanin Manchester da Singha All Stars na Thailand
Dan wasan Manchester Wayne Rooney a lokacin da ya ke sauka da jirgi domin wasan sada zumunci tsakanin Manchester da Singha All Stars na Thailand REUTERS/Chaiwat Subprasom

Kafofin yada labaran Birtaniya sun ruwaito cewa Dan wasan Manchester United Wayne Rooney yana cikin bacin rai game da kalaman Kocin Manchester akan makomar shi. Moyes yace zai iya bukatar Rooney matuka idan har Robin van Persie ya ji rauni, duk da kocin yace yana iya amfani da Rooney da van Persie a lokaci guda kamar yadda zai iya hada Welbeck da Javier Hernandez.

Talla

Amma kalaman na sabon kocin na Manchester sun yi wa Rooney zafi, kamar yadda kafar yada labaran wasanni ta Sky ta ruwaito.

Tun zuwan Robin van Persie, a Manchester Rooney ke cin benci, domin Rooney da aka sani yana ruwan kwallaye a raga amma a kakar da ta gabata dan wasan ya jefa kwallaye 12 ne kacal, inda Van Persie ya jefa kwallaye 30.

Yanzu haka dai jaridun Birtniya sun ce idan Chelsea za ta saye dan wasan sai ta ware kudi Fam Miliyan 80, amma Jaridar The Sun tace Manchester United tafi kaunar ta sayar wa Arsenal daRooney.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.