Tseren Keke

Jaridar L'Equipe ta wanke Froome

Christopher Froome a tserene keken gasar Tour de France
Christopher Froome a tserene keken gasar Tour de France REUTERS/Jean-Paul Pelissier

Jaridar L'Equipe a Faransa, ta kare Chris Froome na Birtaniya wanda ke jagorancin tawagar tseren keken da doruwar riga gasar Tour De France, bayan zargin dan wasan yana kwankwadar kwayu.

Talla

Tun tuni ne dan wasan ya ke karyata tambayoyin ‘yan jaridu ko yana karawa kansa kuzari, saboda yadda ya ke hayewa tsauni a tseren keken.

Amma a wani bincike da jaridar L'Equipe ta gudanar, jaridar ta wanke dan tseren keken bayan ta bi diddigin bayannan gwajin da likitoci suka yi masa a baya.

Jaridar ta taka rawa wajen bankado bayanan da suka tona wa Lance Armstrong asiri a baya wanda har aka haramta masa kofuna bakwai da ya lashe a Tour de France.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.