Kwallon kafa

Mourinho ya tabbatar da niyyarsa ta sayo Rooney daga Manchester United

Sabon Kocin Chelsea Jose Mourinho a lokacin da ake gabatar da shi
Sabon Kocin Chelsea Jose Mourinho a lokacin da ake gabatar da shi REUTERS/Suzanne Plunkett

Jose Mourinho ya fara wani sabon zangon kasancewar a kungiyar Chelsea da samun akan kungiyar Singha All - Stars da ci 1-0 a birnin Bangkok a wani wasan sada zumunci da aka buga. 

Talla

Koda yake wani batu da ya mamaye wannan nasara da Mourinho ya samu shine batun yunkurin sayo dan wasan gaban Manchester United, wato Wayne Rooney akan kudi da aka kimanta ya kai miliyan 11 na kudin euro, wato kwatankwacin kudi dalar Amurka miliyan 15.

Mourinho wanda ya tabbatar da shirin sayen dan wasan ya ce ya rage ga kungiyar ta Manchester united da kuma shi Rooney su yi zabi akan tayin neman sayen dan wasan da suka yi.

Har ila yau yan kara tabbatar da cewa kungiyar ta Chelsea ba ta zawarcin wani dan wasa baya ga Rooney.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.