Kasuwar 'Yan wasa

Suarez da Higuain ba na sayarwa ba ne, United tana farautar Bale

Gareth Bale dan wasan Kungiyar Tottenham
Gareth Bale dan wasan Kungiyar Tottenham Tottenham.com

Kungiyar Real Madrid za ta rike dan wasanta Gonzalo Higuain tare da yin watsi da bukatar sayen Zlatan Ibrahimovic na PSG. Kungiyar Liverpool tace suarez ba na sayarwa ba ne, Manchester United ta fara farautar Gareth Bale, na Tottenham.

Talla

Spain

Jaridar Marca a Spain tace Kungiyar Real Madrid zata rike dan wasanta Gonzalo Higuain wanda Arsenal ke bukata tare da yin watsi da bukatar sayen Zlatan Ibrahimovic na PSG.

Tuni Rahotanni suka ruwaito Carlo Ancelotti yana bukatar sayen Ibrahimovic domin ya biyo shi zuwa Madrid bayan ya baro PSG, amma jaridar Marca tace babu wata tattaunawa mai karfi tsakanin dan wasan da Ancelotti.

Jaridar tace Ancelotti yana bukatar Gonzalo Higuain ya ci gaba da taka kwallo a Real Madrid.

Ingila

Jaridar Daily Mirrow ta ruwaito cewa Manchester United ta fara farautar Gareth Bale na Tottenham wanda ta ware wa kudi Fam miliyan 60 amma jaridar tace yana da wahala Tottehmham ta amince da yarjejeniyar saboda adawa ta fi kaunar ta sayar wa Real Madrid da son dan wasan.

Manchester ta fara neman hanyoyin da za ta maye gurbin Rooney duk da David Moyes ya jajirce dan wasan ba na sayarwa ba ne.

A yau Alhamis Kocin na Manchester ya kauracewa ‘yan jaridu wadanda suke neman ya mayar da martani akan makomar Rooney.

Mourinho ya jajirce akan bukatar sayen Rooney, amma tsohon zakaran dan wasan Manchester Bryan Robson ya cije da bukatar kada Manchester ta sayar da Rooney duk da dan wasan yace yana cikin bacin rai.

Kocin Kungiyar Liverpool Brendan Rodgers yace Luiz Suarez ba na sayarwa ba ne bayan kungiyar ta yi watsi da tayin Arsenal na kudin Fam Miliyan 45.

Dan wasan yana da sauran shekaru uku, yarjejeniyar shi ta kawo karshe a Liverpool, Kuma a kaka mai zuwa dan wasan zai kwashe tsawon makwanni 6 a benci saboda hukuncin laifin cizo da ya aikata.

Dan wasan Faransa kuma Florent Malouda ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da kungiyar Turkiya Trabzonspor, daga Chelsea.

Dan wasan ya kwashe lokaci yana cin benci a Chelsea tun wasan karshe tsakanin Chelsea da Bayern Munich a gasar zakarun Turai kaka biyu da suka gabata.

Manchester City kuma ta sayar da Maicon zuwa Roma wanda City ta saya daga Inter Milan. Shi ma dan wasan ya dade yana cin benci a City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.