Kwallon kafa

Bayern na duba yiwuwar rage ‘yan wasanta

Mai horar da 'yan wasan Bayern Munich, Pep Guardiola
Mai horar da 'yan wasan Bayern Munich, Pep Guardiola Reuters

Hukumomin kungiyra kwallon kafa kungiyar Bayern Munich za su yi wani zama na musamman domin duba yiwuwar rage ‘yan wasa a kungiyar wacce ke dauke da zakarun ‘yan kwallo na duniya.

Talla

Wannan zama da hukumomin ke son yi na zuwa ne a dai dai lokacin da ya rage makwanni biyu kacal a fara fafatawa fagen gasar ta Bundesliga.

Rahotanni na nuna cewa akwai bukatar mai horar da ‘yan wasan, Pep Guardiola ya yi wasu shawarwari na gaggawa musamman ta yadda zai ji da ‘yan wasan kusan goma wadanda duk suna buga tsakiya ne.

“Za mu tattauna akan wannan bayan Super Cup, muna kokarin mu san ‘yan wasan ne a yanzu.” Inji Guardiola.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.