Tseren Keke

Bradley Wiggins zai kara a gasar Tour of Poland

Bradley Wiggins yana gaisawa da magoya bayansa bayan lashe gasar Tour de Franc a bara
Bradley Wiggins yana gaisawa da magoya bayansa bayan lashe gasar Tour de Franc a bara REUTERS/Stephane Mahe

Zakaran da ya lashe gasar Tour de France a bara, Bradley Wiggins zai dawo fagen tsere a karkashin kungiyarshi ta Sky inda zai kara a gasar Tour of Poland. 

Talla

Wiggins bai samu daman kare kambunsa na Tour de France ba saboda fama da ya yi da rashin lafiya wanda hakan ya sa ya fice daga gasar Giro d’Italia a watan Mayu.

Sai dai rahotannin na nuna cewa Wiggins, dan shekaru 33 ya samu sauki kuma zai fara karawa ne a gasar ta Poland.

Masu sharhi da dama na ikrarin cewa rashin halartar Wiggins gasar Tour de France da aka kammala ne ya bawa Chris Froome damar lashe gasar a wannan karo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.