Kasuwar 'Yan wasa

Madrid ta fara tattaunawa da Bale

Dan wasan Tottenham Hostpur  Gareth Bale
Dan wasan Tottenham Hostpur Gareth Bale

Jaridu a Spain sun ruwaito cewa Kungiyar Tottenham ta cim ma yarjejeniya da Valencia akan Roberto Soldado domin maye gurbin Gareth Bale da Real Madrid ke neman zubawa makudan kudade Kamar yadda aka ruwaito kocin Real Madrid Carlo Ancelotti yana tabbatar da cewa sun fara tattaunawa da Tottenham domin mallakar dan wasan.

Talla

A ranar Laraba an an ruwaito dan wasan na Tottenham ya fito horo a cikin tawagar kungiyar wanda Real Madrid ke shirin zubawa makudan kudade.

Kafar yada labaran ta Sky a Birtaniya tace dan wasan ya fice horo bayan ya shaidawa kocin Tottenham Andre Villas-Boas sha’awar shi na komawa Real Madrid.

Dan wasan ya ja hankalin duniya ne saboda tsadar kudi da aka zuba masa Fam Miliyan 80, kudaden da Real Madrid ta zuba wajen sayen Cristiano Ronaldo daga Manchester United.

Jaridar Guardian ta Birtaniya tace Real Madrid a shirye take ta zuba kudi domin sayen dan wasan, yayin da kuma jaridar Marca a Madrid tace Tottenham ta kara ma dan wasan kudi fiye da haka.

A jimlance, kudaden da aka zuba wa dan wasan sun lunka kudaden da aka saye zaratan ‘yan wasa guda biyar a bana da suka hada Mario Gomez da Carlos Tevez da David Villa da Thiago da kuma Jesus Navas.

Tsohon dan wasan Real Madrid Zinedine Zidane, yace idan har Gareth Bale yana da sha’awar zuwa Real Madrid ya dace Tottenham ta basu damar shiga tattaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.