Kwallon Kafa

Arsenal tana neman Benzema da Di Maria na Madrid

Karim Benzema yana tabewa da Di Maria a wasansu da LA Galaxy ta Amurka
Karim Benzema yana tabewa da Di Maria a wasansu da LA Galaxy ta Amurka REUTERS/Ralph D. Freso

Jaridun Birtaniya sun ruwaito cewa Arsenal tana neman sayen Karim Benzema da Angel Di Maria na Real Madrid saboda Gonzalo Higuain da Luis Suarez sun kubucewa Arsene Wenger kocin Kungiyar.

Talla

Har yanzu dan wasa guda ne Arsenal ta saya daga Auxerre, Yaya Sanogo amma rahotanni sun ce akwai kudi Fam Miliyan 100 da aka warewa Wenger domin cefanen ‘yan wasa kafin a rufe kasuwar.

A daren Laraba, Arsenal ta bi Fenerbahce har gida ta lallasa ta ci 3-0 a wasan neman shiga gasar Zakarun Turai kungiyar bayan ‘Yan wasan Gunners sun sha kashi a hannun Aston villa ci 3-1 a ranar farko ta gasar Premier.

Gibbs da Ramsy da Giroud su ne suka zirawa Arsenal kwallayenta a ragar Fenerbahce, wasan da Wenger ya bayyana a matsayin ba sassauci.

Hakan ke nuna Arsenal tana da kwarin giwa a haduwarsu ta gaba a Emirates a makon gobe.

Premier

A Stamford Bridge Kungiyar Chelsea ta sha da kyar ne a hannun Aston Villa ci 2-1 a gasar Premier League da aka gudanar a daren Laraba.

A ranar Litinin mai zuwa ne Chelsea za ta fafata da Manchester United, kafin ta kece raini da Bayern Munich a wasan lashe Super Cup na Turai.

Kafin Chelsea ta kara da United, Mourinho yace baya da wani kudiri na sake tayin dan wasan bayan Manchester ta yi watsi da tayin har sau biyu.

Kodayake yace har yanzu be fitar da rai ba akan dan wasan, sai dai kuma yace zai sassauta bukatar domin kada maganar Rooney ta janye hankalin karawasu da Moyes a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.