Wasanni

Watakila Gareth Bale zai bar Tettenham zuwa Real Madrid

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas  ya rungume Dan wasan shi Gareth Bale
Kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya rungume Dan wasan shi Gareth Bale REUTERS/Eddie Keogh

Kungiyar Tottenham ta kasar ingila na tattaunawa mai karfi da Real Madrid din kasar Spain, kan yuwuwar dan wasa Gareth Bale, ya koma Bernabeu. Har yanzu dai a ba a kai ga cimma matsaya kan wannan cinikin ba, amma ana ganin watakila kudin da za a biya kan dan wasan mai shekaru 24, za su zarta Fam din Ingila Miliyon 80 da Real din suka mika wa Manchester United a shekarar 2009, lokacin da suka sayi Cristiano Ronaldo.