Kasuwar 'Yan wasa

PSG tana neman kwace wa Madrid Gareth Bale

Gareth Bale dan wasan Kungiyar Tottenham
Gareth Bale dan wasan Kungiyar Tottenham Tottenham.com

Jaridun Wasanni a Turai sun ce akwai wasu kungiyoyi da suke neman kwace wa Real Madrid dan wasan Tottenham Gareth Bale, wanda Real ta zubawa makudan kudade fiye da adadin kudin da ta saye Cristiano Ronaldo.

Talla

Rahotanni sun ce Manchester United da PSG sun mika bukatarsu na sayen dan wasan.
Musamman kungiyar PSG ta Balaraben Attajirin kasar Qatar wanda ke zubar da kudi domin zubin sabbin ‘yan wasa.

Tuni rahotanni suka ce dan wasan har ya isa Spian amma kocin Tottenham Andre Villas-Boas yace yana tsammanin dan wasan zai dawo horo ranar Talata kafin a kawo karshen yarjejeniyar.

An tambayi David Moyes game da ko Manchester tana neman saye Bale, kocin yace a’a amma be karyata bukatarsu ba na neman dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.