Kwallon Kafa

Ferguson ya fara fuskantar suka

Tsohon Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson tare da Luis Nani
Tsohon Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson tare da Luis Nani

Bayan kaddmar da littafin rayuwar Sir Alex Ferguson na Manchester United, mai tsaron gida dan kasar Australia Mark Bosnich da Ferguson ya horar yace yana son ya hadu da tsohon kocin na Manchester domin kalubalantar shi.

Talla

A jiya Talata ne aka kaddamar da litattafin rayuwar Ferguson kuma a cikin litattafin Ferguson ya bayyana sunan Bosnich a matsayin Ja’iri wanda baya ganin mutunci mutane.

Bayan kammala kakar da ta gabata ne Ferguson ya yi ritaya bayan ya lashe kofuna 13 a Manchester.

Bosnich wanda yanzu ke aiki da wata kafar Telebijin yace yana fatar zai hadu da Ferguson domin kalubalantar shi akan yadda kocin ya yi watsi da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.