Champions League

Munich da PSG sun yi ruwan kwallaye a raga

Zlatan Ibrahimovic na PSG a lokacin da ya ke jefa kwallo a ragar Anderlecht a gasar Zakarun Turai
Zlatan Ibrahimovic na PSG a lokacin da ya ke jefa kwallo a ragar Anderlecht a gasar Zakarun Turai REUTERS/Francois Lenoir

Bayern Munich da Paris Saint-Germain sun yi ruwan kwallaye a wasannin da suka fafata na gasar zakarun Turai, kamar yadda Real Madrid da Manchester United suka lashe wasanninsu.

Talla

Bayern Munich ta lallasa kungiyar Viktoria Pilsen ne ta Jamhuriyyar Czech ci 5-0. Kuma Ribery da Alaba da Schweinsteiger su ne suka zira wa Guardiola kwallayen a raga.

Yanzu haka Bayern Munich tana jagorancin teburin rukuninsu ne na D da tazarar maki 3.

Manchester City kuma ta sha da kyar ne a kasar Rasha bayan ta doke CSKA Moscow ci 2-1.

A Brussels, PSG ta caccasa Anderlecht ne ci 5-0, Kuma Zlatan Ibrahimovic ne ya jefa kwallaye 4 a raga, sai Edinson Cavani wanda ya jefa kwallo daya.

A rukuninsu na C Benfica da Olympiakos sun yi kunnen doki ne ci 1-1, wanda ya ba PSG damar jagorancin teburin rukunin da maki 5.

A Santiago Bernabeu, Real Madrid ta doke Juventus ci 2-1 kuma Cristiano Ronaldo, ne ya kada kwallayen a raga. Yanzu dan wasan yana da jimillar kwallaye 7 a gasar zakarun Turai.

Har yanzu Juve ba ta samu maki guda ba, yayin da Real Madrid ke jagorancin rukuninsu na B.

Kungiyar Galatasaray ta Turkiya ta doke FC Copenhagen ci 3-1, Wesley Sneijder da Didier Drogba ne suka jefa kwallayen a raga.

Manchester United kuma ta samu sa’ar Real Sociedad ne ci 1-0 a Old Trafford kwallon da Inigo Martinez na Sociedad ya ba David Moyes.

Yanzu United ce saman teburin rukuninsu da tazarar maki daya tsakaninta da Bayer Leverkusen, wacce ta lallasa Shakhtar Donetsk ci 4-0 a kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI