Tennis

Nadal da Djokovic da Federer sun lashe wasanninsu a Paris Masters

Roger Federer a lokacin da ya ke karawa a gasar Grand Slam ta US Open
Roger Federer a lokacin da ya ke karawa a gasar Grand Slam ta US Open REUTERS/John Sommers II

Rafael Nadal da Novak Djokovic da Roger Federer dukkaninsu sun tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a gasar Paris Master, wadanda birnin London zai karbi bakuncinsu a gasar duniya ta ATP.

Talla

Zakaran Tennis din na duniya Nadal ya doke Jerzy Janowicz, Novak Djokovic kuma ya doke dan wasan Amurka John Isner yayin da kuma Federer, ya lallasa Philipp na Jamus.

Nan gaba, Djokovic zai kara ne tsakanin shi da Wawrinka wanda ya lallasa a gasar Australian Open da US Open a bana.

Nadal zai kara ne tsakanin shi da Gasquet a zagayen kwata Fainal. Federer kuma wanda ya lashe kofunan Grand Slams guda 17 zai kara ne da Del Potro na Argentina wanda ya doke Dimitrov na Bulgeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.