Faransa

An hada PSG wasa da Saint-Etienne a Faransa

An hada kungiyoyin da zasu kara da juna a zagaye na biyu a gasar neman lashe kofin kasar Faransa. Kuma akwai barazana ga PSG domin zata kara ne da Saint-Etienne da ke rike da kofin gasar.   A bara, PSG ta sha kashi ne a hannun Saint-Etienne a wasan dab dana karshe.

Saint-Etienne, tana barje gumi da  PSG a gasar cin kofin Faransa
Saint-Etienne, tana barje gumi da PSG a gasar cin kofin Faransa REUTERS/Robert Pratta
Talla

Kungiyar Lyon zata kara ne da Reims, Nantes kuma ta kece raini daAuxerre.

An hada Marseille da Toulouse, Evian da Bastia, Rennes da Bordeaux.

A daya bangaren kuma Kocin Faransa ya kira dan wasan Manchester United Patrice Evra cikin tawagar ‘Yan wasa 24 da za su fafata da Ukraine a wasan neman tsallakewa zuwa gasar cin kofin Duniya a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI