Kwallon Kafa

Manchester United za ta karbi bakuncin Arsenal

Robin van Persie na Manchester United da Mesut Ozil na Arsenal
Robin van Persie na Manchester United da Mesut Ozil na Arsenal Eurosport

A ranar Lahadi hankali zai koma ga wasa tsakanin Manchester United da Arsenal a filin wasa na Old Trafford a gasar Premier League ta Ingila, inda a bana Arsenal ce ke jagorancin Teburin gasar. Hakan ke nuna Arsene Wenger ya nuna shirye ya ke a bana bayan kwashe shekaru 8 ba tare da lashe kofi ba.

Talla

A Ranar Assabar Akwai wasa tsakanin:

Aston Villa da Cardiff City

Chelsea da West Bromwich Albion

Crystal Palace da Everton

Liverpool da Fulham

Norwich City da West Ham United

A ranar Lahadi akwai wasa tsakanin:

Tottenham Hotspur da Newcastle United

Sunderland da Manchester City

Swansea City da Stoke City

Faransa

Laurent Blanc bayan ya kalubalanci ‘Yan wasan shi na PSG na rashin nuna bajinta a wasannin da suka gabata na baya baya nan, yace yana fatar samun sauyi daga ‘Yan wasan a ziyarar da kungiyar Nice zata kawo masu.

A ranar Talata PSG ta yi kunnen doki ne tsakaninta da Anderlecht a gasar zakarun Turai, kodayake tun fara kakar bana ba’a samu galabar PSG ba amma kungiyar na neman tazara ne tsakaninta da Monaco da Lille a teburin league din Faransa.

A yau Juma’a, Monaco zata fafata ne da Evian, inda zata nemi huce hushin kashin da ta sha a karshen makon jiya a hannun Lille ci 2-0.

PSG ce ke jagorancin Tebur, Lille ce ke bi mata sai kuma Monaco a matsayi na uku.
A gobe Assabar Paris Saint-Germain za ta kara ne da Nice. A ranar Lahadi kuma akwai kallo tsakanin Saint-Etienne da Lyon.

Sauran wasannin sun hada da:

Bastia da Rennes

Guingamp da Lille

Lorient da Reims

Toulouse da Ajaccio,

Valenciennes da Montpellier

A ranar Lahadi akwai wasa tsakanin:

Bordeaux da Nantes

Marseille da Sochaux

Spain

A La liga a Spain, ido zai dawo ne ga tsadadden dan wasan duniya Gareth Bale a lokacin da Real Madrid zata karbi bakuncin Real Sociedad bayan ya zira kwallo a ragar Juventus da aka tashi ci 2-2 a gasar zakarun Turai.

A wasanni biyu da suka gabata Bale ya zira kwallaye biyu a La liga tare da taimakawa Ronaldo da Benzema jefa kwallo a raga.

A bana, Ronaldo ya samu jimillar kwallaye 222 a wasanni 215 ya buga wa Real Madrid.

Real Madrid na iya datse tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona da kuma Atletico Madrid idan har ta samu nasara a gobe Assabar kafin Barca a Atletico su buga wasanninsu a ranar Lahadi.

Barcelona zata kai wa Real Betis ziyara ne bayan sun doke AC Milan ci 3-1 a gasar zakarun Turai.

Atletico Madrid kuma da ta lallasa Austria Vienna a gasar zakarun Turai ci 4-0 zata kara ne da Villareal da ke a matsayi na hudu a Teburin La liga.

Bundesliga

A Bundesliga ta kasar Jamus, Bayern Munich zata buga wasanni 37 ne ba tare da samun galabarta ba a bana idan har ta doke Augsburg, ko suka yi kunnen doki a karshen mako a filin wasan Allianz Arena.

Bayern ta kafa tarihi ne kamar yadda Hamburg ta kafa na buga wasanni 36 ba tare da samun galabarta ba a shekarar 1983, bayan Bayern Munich ta doke Hoffenheim ci 2-1 a ranar Assabar.

Bayern Munich ce ke jagorancin Teburin Bundesliga, amma Borussia Dortmund da ke a matsayi na biyu zata nemi hucewa ne akan Wolfsburg bayan ta sha kashi a hannun Arsenal a gasar zakarun Turai

Seria A

A Seria a kasar Italiya, Kungiyar Roma da ke jagorancin Teburin gasar zata karbi bakuncin sabuwar kungiyar da ta shigo gasar a bana Sassualo a ranar Lahadi yayin da daga bisani kuma a kece raini tsakanin Juventus da Napoli.

Akwai wasa tsakanin:

Chievo da Milan

Parma da Lazio

Fiorentina da Sampdoria

A ranar Assabar akwai wasa tsakanin:

Catania da Udinese

Inter da Livorno

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.