FIFA

New Zealand da Jordan sun sha kashi

‘Yan wasan All White na New Zealand sun sha kashi a hannun Mexico ci 5-1 a fafatawa ta farko a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da aka gudanar a jiya Laraba tsakanin kasashen yankin Asiya da kudancin Amurka.

Rafael Marquez na Mexico yana murnar zira kwallo a ragar New Zealand
Rafael Marquez na Mexico yana murnar zira kwallo a ragar New Zealand REUTERS/Henry Romero
Talla

Jaridun kasar New Zealand a yau Alhamis wannan labarin ne ya mamaye kanun labaransu, inda kusan daukacin jaridun kasar suka ce hakan ya nuna babu wata alamar New Zealand na iya kai ziyara zuwa kasar Brazil a badi.

Haka ma kasar Uruguay ta lallasa kasar Jordan ne 5-0 a fafatawar neman zuwa kasar Brazil a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI