FIFA

Za’a tankade Ronaldo ko Ibrahimovic zuwa Brazil

Zaratan ‘Yan wasa guda biyu a Turai da za’a iya hasarar guda daga cikinsu a Brazil tsakanin Cristiano Ronaldo na Portugal da Zlatan Ibrahimovic wadanda za su kece raini da juna a gobe Juma’a a wasan neman shiga gasar Cin kofin duniya.

Cristiano Ronaldo na Portugal
Cristiano Ronaldo na Portugal REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Ronaldo da Ibrahimovic ‘yan wasa ne da suka san sirrin raga domin a karshen mako ko wannensu ya zira kwallaye uku a raga inda Ronaldo ya jefa kwallaye uku a wasan da Real Madrid ta lallasa Real Sociedad ci 5-1, Ibrahimovic kuma ya zira kwallaye uku a ragar Nice da aka tashi wasan ci 3-0.

Sweden da Portugal sun kasance ne a matsayi na biyu a rukunin kasashen da aka hada su tun a tashin farko. sai dai kuma dole a badi sai an yi gasar cin kofin duniya ba tare da daya daga cikinsu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI