Kwallon kafa

Jamus ta mamayi Ingila da ci 1-0 a Wembley

Mai horar da 'yan wasan Igila Roy Hodgson
Mai horar da 'yan wasan Igila Roy Hodgson

Jamus ta doke Ingila da ci 1-0 a wasan sada zumunci da aka buga jiya a filin Wembley. Wannan kuma shine karo na biyu da ake doke Ingila a ‘yan kawanakin inda Chile ta lallasa tad a ci 2-0 a ranar Juma’ar da ta gabata.

Talla

Wannan shine karo na farko tun bayan shekarar 1977 da kasar ta samu irin wannan koma baya a cikin gida.

Sai dai mai horar da ‘yan wasan, Roy Hodgson ya ce hakan ba mizani ne da za dora kan rawar da Ingilan za ta taka a gasr cin kofin duniya a badi.

Sauran sakamakon wasanni sada zumunci, Poland da Jamhuriyar Ireland sun ta shi canjaras, wato 0-0, Austria ta doke Amurka da ci daya da nema, yayin da itama Slovenia ta lallasa Canada da ci 1-0.

Afrika ta Kudu ta doke zakarun duniya, wato Spain da ci 1-0 sannan Netherland da Colombia sun tashi canjaras.

Haka zalika Japan ta doke Belgium da ci 3-2, Turkiya ta lallasa Belarus da ci 2-1 sannan Australia ta mamayi Costa Rica da ci 1-0.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.