Kwallon kafa

Gwamnatin Jihar Kano ta yiwa ‘yan wasan Golden Eaglets goma ta arziki

Matasan Najeriya suna murnar lashe kofin gasar cin kofin 'Yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na Mohammed Bin Zayed a Abu Dhabi
Matasan Najeriya suna murnar lashe kofin gasar cin kofin 'Yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na Mohammed Bin Zayed a Abu Dhabi REUTERS/Ahmed Jadallah

Gwamnatin Jihar kano ta karrama ‘yan wasan Golden Eaglets da suka lashe gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 a jiya Talata inda ta yiwa kowane dan wasa alkawarin kudi naira 300,000.00 yayin da mai horar da su, Manu Garba zai samu 500,000.00.

Talla

Gwamnan Jihar Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a wani bikin karrama ‘yan wasa da aka shirya ya yiwa ‘yan asalin kano dake tawagar kungiyar su biyu, wato Zahraddeen Bello da Musa Muhammad alkwarin gidaje.

Haka zalika za a saka sunayen ‘yan wasa a wasu titunan birnin na Kano.

A baya gwamnatin tarayya ta karrama ‘yan wasan da kyautar kudi miliyan biyu –biyu.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI