Kwallon kafa

Monaco ta lallasa Nice da ci 3-0, Dortmund ta shiga zagayen quarter- final a German Cup

Lucas Ocampo dan wasa Monaco
Lucas Ocampo dan wasa Monaco Reuters/Eric Gaillard

A gasar Faransa kuwa a jiya Nantes ta doke Valencienne da ci 2-1 Lille ta lallasa Marseille da ci 1-0 yayin da Monaco ta doke Nice da ci 3-0. A yau kuma Ajjacio za ta kara da Bastia, Guingamp za ta kara da Bordeaux, PSG ta kaiwa Evian ziyara sannan Rennes ta karbi bakuncin Saint Etienne. 

Talla

A kasar Jamus kuwa, Borussia Dortmund ta shiga zagayen quarter final a gasar German Cup yayin da Schalker 04 ta fice daga gasar bayan ta sha kashi a hanun Hoffeinham da ci 3-1.

A yau kuma Bayern Munich wacce ke rike da kofin za ta fafata da Ausburg.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.