Champions League

City ta doke Bayern, Ronaldo ya kafa Tarihi

Cristiano Ronaldo tare da abokan wasan shi a Real Madrid suna murnar zira kwallo a ragar FC cofenhagen a gasar zakarun Turai inda ya kafa tarihin wanda ya fi yawan zira kwallaye a raga a zagayen Farko bayan ya zira kwallaye 9
Cristiano Ronaldo tare da abokan wasan shi a Real Madrid suna murnar zira kwallo a ragar FC cofenhagen a gasar zakarun Turai inda ya kafa tarihin wanda ya fi yawan zira kwallaye a raga a zagayen Farko bayan ya zira kwallaye 9 EUFA

Manchester City ta doke Bayern Munich ci 3-2 a gasar zakarun Turai a daren jiya, inda Sai da Bayern Munich ta fara zira wa City kwallaye biyu a raga amma daga bisani City ta rama kwallayen tare da jefa kwallo ta uku.

Talla

Wannan ne karo na farko da Pep Guardiola ya sha kashi tun lokacin da ya karbi aikin horar da Bayern Munich mai rike kofin gasar zakarun Turai yanzu haka.

Tuni dukkanin kungiyoyin biyu suka tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar a rukuninsu da D, amma Bayern Munich ce ke saman teburin rukunin da maki 15.

Bayer Leverkusen ma ta tsallake zuwa zagaye na biyu a rukunin A bayan ta doke Real Sociedad 1-0. Haka ma Olympiakos ta tsallake bayan ta lallasa Anderlecht ci 3-1 a rukunin C.

A rukunin B da Real Madrid ke jagoranci har yanzu akwai sauran fafatawa domin a jiya dussar kankara da ke zuba ta sa an dakatar da wasa tsakanin Galatasaray da Juventus har zuwa yau Laraba.

Juventus tana neman kunnen doki ne kafin ta tsallake zuwa zagaye na biyu.

Real Madrid kuma ta doke Copenhagen ta Denmark 2-0 inda Cristiano ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya jefa kwallaye 9 a zagayen farko. Ronaldo yanzu ya sha gaban Ruud Van Nistelrooy da Filippo Inzaghi da Hernan Crespo da suka jefa kwallaye 8 a raga.

Mancheester United da ta sha kashi a Premier League ta samu nasara ne akan Shakhtar Donetsk ta Ukraine ci 1-0.

Kungiyar Benfica kuma ta ga samu ne ta ga rashi saboda duk da cewa ta doke PSG ci 2-1 amma kungiyar ta fice gasar zakarun Turai saboda nasarar da Olympiacos ta samu akan Anderlecht.

A yau Laraba kuma za’a ci gaba da gasar zakarun Turai inda Schalke 04 zata fafata da Basel

A London kuma Chelsea zata karbi bakuncin Steaua Bucarest ta Romania.
Marseille ta Faransa zata kara ne da Borussia Dortmund ta Jamus, yayin da Napoli zata karbi bakuncin Arsenal.

A birnin Vienna, kungiyar Austria Vienna zata kara ne da Zenit Saint-Petersbourg ta Rasha. Yayin da Atletico Madrid ta Spain ta kece raini tsakaninta da FC Porto Portugal.

A rukunin H, AC Milan zata karbi bakuncin Ajax ne ta Holland, FC Barcelona kuma ta kece raini da Celtic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.