EUFA

Neymar ya jefa kwallaye uku a raga

Kungiyar AC Milan ita ce kungiyar tilo daga Italiya da ta samu rayuwa a gasar zakarun Turai bayan an tashi wasa tsakaninta da Ajax babu ci a San Siro. A karon farko Neymar na Brazil ya yi wa Barcelona ruwan kwallaye uku inda ya taimakawa kungiyar lallasa Celtic shi 6 da 1.

Neymar na Barcelona yana sumbatar kwallo bayan ya jefa kwallaye uku a ragar Celtic a gasar zakarun Turai a filin wasa na Camp Nou
Neymar na Barcelona yana sumbatar kwallo bayan ya jefa kwallaye uku a ragar Celtic a gasar zakarun Turai a filin wasa na Camp Nou REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Tuni Juventus ta fice gasar bayan ta sha kashi a hannun Galatasaray ta Turkiya ci 1-0 a birnin Istanbul.

Galatasaray ce ta samu nasarar tsallakewa a rukuninsu na B inda take bi wa Real Madrid da ke jagorancin Teburinsu.

Napoli ma an yi waje da ita ne duk da cewa ta samu maki daya da Arsenal da Borussia Dortmund.

A daren jiya laraba Napoli ta doke Arsenal ne ci 2 da 0 a rukuninsu na F yayin da Borussia Dortmund ta doke Marseille 2 da 1 a Faransa.

Duk da dai Arsenal ta sha da kyar ne amma wannan ne karo na 14 da kungiyar ke tsallakewa zuwa zagaye na biyu a jere a gasar zakarun Turai.

A karon farko Neymar na Brazil ya yi wa Barcelona ruwan kwallaye uku inda ya taimakawa kungiyar lallasa Celtic shi 6 da 1. Yanzu Neymar ya zira kwallaye 5 ne a wasanni 20 tun zuwansa Barcelona.

Schalke 04 ma ta tsallake zuwa zagaye na biyu bayan ta doke FC Basel ci 2 da 0, Schalke 04 ce ke bi ma Chelsea da ta jagoranci teburin rukuninsu.

A birnin London Chelsea ta doke Steaua Bucharest ta Romania ci 1-0. A Birnin Vienna kuma Austria Vienna ta lallasa Zenit St. Petersburg ta Rasha ci 4-1. Yayin da Atletico Madrid ta Spain da doke FC Porto ta Portugal ci 2 da 0

Kungiyoyin da suka tsallake wadanda suka jagoranci teburin rukuninsu sun hada da :

Manchester United (Ingila)

Real Madrid (Spain)

Paris Saint-Germain (Faransa)

Bayern Munich (Jamus)

Chelsea (Ingila)

Borussia Dortmund (Jamus)

Atletico Madrid (Spain)

Barcelona (Spain)

Wadanda suka tsallake a matsayi na biyu sun hada da :

Bayer Leverkusen (Jamus)

Galatasaray (Turkiya)

Olympiakos (Girka)

Manchester City (Ingila)

Schalke (Jamus)

Arsenal (Ingila)

Zenit St Petersburg (Rasha)

AC Milan (Italiya)

A ranar Litinin din makon gobe ne za’a hada kungiyoyin da zasu kara da juna a zagaye na biyu bayan kammala zangon farko a jiya Laraba.

Kungiyoyin da suka fito a rukuni daya ba zasu hadu da juna ba haka kuma kungiyoyin da suka fito a kasa daya ba zasu hadu ba a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI