Kwallon Kafa

Inter ta sha kashi, Villas-Boas yace ba zai yi murabus ba

Carlos Tevez ya jefa kwallaye uku a raga inda ya taimakawa Juventus lallasa Sassuolo ci 4-0 a Seria A bayan ta sha kashi ci 1-0 a hannun Galatasaray a gasar zakarun Turai. A daren yau Litinin ne Roma zata kai wa AC Milan ziyara a San Siro.

Luis Suarez na Liverpool wanda ya jefa kwallaye a ragar Tottenham
Luis Suarez na Liverpool wanda ya jefa kwallaye a ragar Tottenham REUTERS/Toby Melville
Talla

Juventus ce ke jagorancin Teburin Seria A da maki shida yayin da Napoli ta lallasa Inter Milan ci 4-2 a karshen mako.

Ingila

A Premier League, Manchester United da Liverpool sun yi ruwan kwallaye ne a karshen mako inda Manchester ta doke Aston Villa ci 3-0 yayin da Liverpool ta lallasa Tottenham ci 5-0.

Arsenal kuma da ke jagorancin teburin gasar ta sha kashi ne ci 6-3 a hannun Manchester City.

Liverpool ce yanzu ke bi wa Arsenal a teburin Premier da yawan kwallaye tsakaninta da Chelsea da ke a matsayi na uku bayan ta doke Crystal Palace ci 2-1.

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas yace ba zai yi murabus ba bayan kwashe makwanni yana shan kashi. A bana Tottenham ta sha kashi a hannun West Ham ci 3-0, kamar yadda Manchester City ta lallasa ta ci 6-0 amma kocin yace hankalin shi zai koma ne ga daidaita al’amurra a kungiyar.

Spain

A La liga har yanzu Atletico Madrid ce ke hamayya ne da Barcelona a teburin gasar inda Diego Costa ya taimakawa kungiyar doke Valencia ci 3-0 a jiya Lahadi.

Neymar na Brazil ne ya jefa wa Barcelona kwallaye biyu a ragar Villarreal da aka tashi wasan ci 2-1.

Barcelona da Atletico, dukkaninsu suna da maki 43 a saman teburin La liga yayin da suka ba Real Madrid tazarar maki 5 bayan Osasuna ta rike Los Blancos ci 2-2 a ranar Assabar.

Yanzu haka Cristiano Ronaldo da Diago Costa ne ke da yawan kwallaye 17 a La liga.

A jiya Lahadi Cristiano Ronaldo ya bude wani gidan tarihi a garin Madeira, da aka haife shi a Portugal inda dan wasan ya zuba kofuna da kyautukan da ya lashe, hadi da kyautar gwarzon dan wasan duniya da ya lashe yana Manchester a 2009.

Faransa

A League 1, dan wasan Cote d’Ivoire Salomon Kalou shi ne ya taimakawa Lille doke Bastia ci 2-1 inda dan wasan jefa kwallaye biyu a raga.

A jiya Lahadi, an tashi wasa ne ci 2-2 tsakanin Lyon da Marseille inda PSG ta ba Marseille tazarar maki 15 teburin gasar a Faransa.

PSG ta doke Rennes ne ci 3-1, kuma Marseille ta koma matsayi na shida ne a Tebur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI