Kwallon Kafa

Inter ta doke Milan, Ancelotti yace yana iya lashe La liga

Dan wasan Inter Rodrigo Palacio a lokacin da ya jefa kwallo a ragar AC Milan a Seria A
Dan wasan Inter Rodrigo Palacio a lokacin da ya jefa kwallo a ragar AC Milan a Seria A REUTERS/Alessandro Garofalo

Kungiyar Inter Milan ta samu sa’ar takwaranta AC Milan ci 1-0 a ranar lahadi, inda wannan nasarar ta ba Inter nasarar haurowa zuwa matsayi na 5 a teburin gasar amma tazarar maki 15 tsakanina da Juventus da ke saman teburin Seria A.

Talla

AC Milan a bana tana matsayi na 13 a yanzu, tazarar maki 17 tsakaninta da Juventus. Saura minti 20 a kammala wasa ne dan wasan Inter Palacio ya jefa wa Inter kwallo a ragar Milan.

Spain

A La liga a Spain Carlo Ancelotti kocin Real Madrid yace yana iya lashe kofin gasar a bana duk da akwai tazarar maki 5 tsakanin shi da Barcelona da Atletico Madrid bayan Real Madrid ta doke Valencia ci 3-2 a jiya Lahadi.

Tuni Barcleona ta doke Getafe ci 5-2 inda Pedro ya zirara kwallaye uku bayan Getafe ta fara zira kwallaye biyu a ragar Barcelona. Atletico Madrid ta sha da kyar ne a hannun Lavente ci 3-2.

Yanzu haka a La liga Diego Costa na Atletico Madrid shi ke da yawan kwallaye 19 fiye da Cristiano Ronaldo na Madrid mai yawan kwallaye 18 a raga.

Faransa

A League 1 kungiyar Lille ta rike PSG ci 2-2 a jiya Lahadi inda tun a ranar Juma’a ne Monaco ta sha kashi ci 2-1 a hannun Valenciennes inda Rademel Falcao ya barar da Fanalty.

Ingila

A Premier league a ingila a yau Litinin, Arsenal tana iya karbe matsayinta na jagorancin teburin gasar idan har ta samu sa’a akan Chelsea a filin wasa na Emirates.

Yanzu haka Liverpool ce ke saman teburn Premier da maki 36 bayan ta lallasa Cardiff City ci 3-1 a ranar Assabar. Manchester City ce ke bi mata a matsayi na biyu inda ta doke Fulham ci 4-2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI