Isa ga babban shafi
Masar

An dawo da wasannin kwallon kafa a Masar

Filin wasan Port Said inda aka smau rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin Al Ahly  da Al Masry a Masar
Filin wasan Port Said inda aka smau rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin Al Ahly da Al Masry a Masar
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

A kasar Masar an dawo da harakokin wasannin kwallon kafa bayan dakatar da wasannin shekaru biyu da suka gabata sakamakon mummunan rikicin da ya faru a filin wasa na Port Said da kuma rikicin siyasa a kasar.

Talla

A watan Fabrairun 2012 ne aka dakatar da wasannin kwallon kafa a Masar bayan wani rikici tsakanin magoya bayan Al Masry da Al Ahly inda mutane sama da 70 suka mutu a filin wasa na Port Said.

A jiya Talata ne dai aka fara fafatawa a wasannin league din kasar tsakanin kungiyar Petrojet da Talae al-Geish, wadanda suka tashi kunnen doki.

Sai dai duk da haka wasannin an gudanar da su ne ba tare da ‘yan kallo ba kuma haka za’a ci gaba da wasannin har sai an samu kwanciyar hankali a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.