Kwallon Kafa

PSG tana nazarin sayen Messi

Kungiyar Paris Saint-Germain ta fara nazarin kudaden da zata ware domin mallakar Lionel Messi na Barcelona kamar yadda jaridun Faransa suka ruwaito. Jaridar Le Parisien tace PSG tana cikin jerin kungiyoyin da za su iya ware kudi euro Miliyan 250 domin cinikin Messi.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya dafe baki bayan sun sha kashi a hannun Real Madrid a filin wasa na Nou Camp a gasar Copa Del Ray
Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya dafe baki bayan sun sha kashi a hannun Real Madrid a filin wasa na Nou Camp a gasar Copa Del Ray REUTERS/Albert Gea
Talla

Jaridar ta yi tsokaci akan rashin fahimtar juna da ke tsakanin Messi da Javier Faus na Barcelona akan sabunta kwangilar shi da batun haraji tsakanin dan wasan da mahukuntan Spain.

Jaridar kuma tace Messi ya shiga damuwa saboda zuwan Neymar da zai iya shafe sunan shi a Barcleona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI