Kwallon Kafa

League Cup: PSG zata buga wasan karshe

Dan wasan PSG  Zlatan Ibrahimovic
Dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic REUTERS/Gonzalo Fuentes

Zlatan Ibrahimovic, ya taimakawa kungiyar PSG tsallake wa zuwa buga wasan zagayen karshe a gasar lashe kofin league din gida a Faransa bayan dan wasan na kasar Sweden ya zirara kwallaye biyu a ragar Nantes inda aka tashi ci 2-1.

Talla

Tun ana minti biyar da fara wasa ne Ibrahimovic ya jefa kwallo ta farko kafin daga bisani dan wasan Nantes Oliviar ya barke kwallon.

Ana dab da kammala wasan ne kuma Ibrahimovic ya sake jefa kwallo ta biyu a raga, Kwallon shi ta 31 a kakar wasan bana

A watan Afrilu ne za’a yi fafatwar karshe.

PSG zata jira ne har zuwa yau Laraba domin sanin kungiyar da zasu fafata a wasan karshe tsakanin Lyon da Troyes wadanda zasu kece raini idan an jima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.