Faransa

Lyon zata hadu da PSG a fafatawar karshe

'Yan wasan Lyon Bafetimbi Gomis da Jimmy Briand suna farin cikin zirara kwallo a ragar Troyes
'Yan wasan Lyon Bafetimbi Gomis da Jimmy Briand suna farin cikin zirara kwallo a ragar Troyes REUTERS/Robert Pratta

Kungiyar Lyon ita ce zata kara da Paris Saint Germain a wasan karshe domin lashe kofin league din gida a Faransa bayan a jiya Laraba ta Lyon ta doke Troyes ci 2 da 1. Tuni PSG ta doke Nantes a ranar Talata a zagayen dab da na karshe. Rabon da Lyon ta lashe kofin tun a 2001 kuma sau uku kungiyar na shan kashi a wasan karshe.

Talla

A bana haduwarta da PSG a wasan karshe babban kalubale ne a gabanta domin ko a watan Disemba PSG ta lallasa ta ci 4-0 a gasar League 1.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne kungiyar biyu zasu fafata a wasan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.