Faransa

Monaco ta doke Nice

Radamel Falcao Dan wasan gaba na Monaco
Radamel Falcao Dan wasan gaba na Monaco francetvinfo.fr

Manaco ta tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a gasar lashe kofin Faransa bayan ta samu sa’a akan Nice ci 1 da 0. Ana dab da kammala wasa ne Dan wasan Monaco Dimitar Berbatov ya jefa ƙwallo a ragar Nice wanda ya ba ƙungiyar nasara a jiya Laraba. A daya bangaren Rennes ita ma ta sha da ƙyar ne a karawarta da Auxerre ci 1-0. Yayin da a yau Alhamis Lyon, zata fafata da Lens.