Premier League

Arteta yace Arsenal zata farfado

Dan wasan Arsenal Mikel Arteta
Dan wasan Arsenal Mikel Arteta

Dan wasan Arsenal Mikel Arteta ya nemi afuwar magoya bayansu akan dukan da Chelsea ta yi masu ci 6-0 a premier league inda Arsene Wenger bai sha da dadi ba wanda a karawar ce a ranar Assabar ya yi haskawa karo na 1,000 a matsayin kocin Arsenal.

Talla

Kashin da Arsenal ta sha a Stamford Bridge shi ne karo na uku da ake lallasa kungiyar a bana bayan ta sha kashi ci 5-1 a hannun Liverpool tare da shan kashi ci 6-3 a hannun Manchester City.

Cikin minti 17 Chelsea ta jefa kwallaye uku a ragar Arsenal, amma rudanin da alkalin wasa ya haifar a wasan shi ne ya ja hankalin mutane a Stamford Bridge.

Alkalin wasa Andre Marriner ya ba Kieran Gibbs jan kati ne maimakon Alex Oxlade-Chamberlain dan wasan da ya tare kwallo da hannu a ragar Arsenal.

Arteta ya sha alwashin zasu wartsake duk da kashin da suka sha a hannun Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.