Spain

Clasico: Barcelona da Real Madrid zasu sake karawa

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi yana kokarin tsira da kwallo a tsakanin 'Yan Real Madrid Xavi Alonso da Luka Modric a karawar Clasico
Dan wasan Barcelona, Lionel Messi yana kokarin tsira da kwallo a tsakanin 'Yan Real Madrid Xavi Alonso da Luka Modric a karawar Clasico Reuters

A yau Laraba ne za’a yi fafatawar Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid inda za’a sake kece raini a bana a wasan karshe na neman lashe kofin gasar Sarki ko Copa del Ray. A karawar da kungiyoyin biyu da suka yi a La liga, Barcelona ce ta samu nasara akan Real Madrid da ci 4 da 3, fafatawar da ba a taba gani ba a Santiago Bernabeu.

Talla

A bana wannan kofin shi ne gaban Barcelona bayan an yi waje da ita a gasar zakarun Turai, kuma fatanta na lashe kofin La liga ya dushe, yayin da Real Madrid ke da yakinin lashe kofuna uku a bana.

A karshen makon nan Barcelona ba ta sha dadi ba a hannun Granada a La liga, kuma wannan dukan shi ya nutse kungiyar a teburin gasar zuwa matsayi na uku.

Real Madrid ita ce a matsayi na biyu, kuma yanzu haka tana cikin kungiyoyi hudu da suka rage a gasar zakarun Turai.

A bana, Barcelona na fuskantar barazana idan har ba ta lashe kofi a yau ba, domin a nan gaba tana iya mikawa Real Madrid kofin La liga idan har ta doke Atletico Madrid a fafatawar karshe, in har kuma Real ta samu nasara a sauran wasanninta da suka rage.

A karawar Clasico a yau Laraba, kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya tabbatar da cewa za’a yi karawar ne ba tare da zakaran kwallon Duniya na bana Cristiano Ronaldo ba saboda rauni da ya samu.

Amma kocin yace rashin dan wasan ba zai hana masu ba Barcelona mamaki ba, ta la’akari da wasa guda aka samu galabarsu a wasanni 10 da suka buga ba tare da Ronaldo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.