UEFA

Zakarun Turai: Chelsea ta rike Atletico

Mai tsaron Gidan Chelsea Petr Cech zai kwashe lokaci yana jinya bayan ya yi karo da dan wasan Atletico Raul Garcia a fafatawar zakarun Turai.
Mai tsaron Gidan Chelsea Petr Cech zai kwashe lokaci yana jinya bayan ya yi karo da dan wasan Atletico Raul Garcia a fafatawar zakarun Turai. REUTERS/Sergio Perez

Wasa tsakanin Atletico Madrid da Chelsea an tashi ne babu ci a karawa ta farko da aka yi a gidan Atletico a gasar zakarun Turai. Amma Chelsea ba ta ci riban wasan ba domin bayan babu ci, kuma mai tsaron gidanta Petr Cech ya tafi jinya da jagoran kungiyar John Terry.

Talla

Haka kuma Frank Lampard da John Obi Mikel na Najeriya ba da su za’a yi karawa ta biyu ba a Stamford Bridge saboda katin gargadi biyu da ke kan wuyansu.

Chelsea dai na iya samun kwarin giwa saboda magoya bayanta da za’a yi karawa ta biyu a gidanta, amma barnar da zata auku shi ne idan Atletico ta fara jefa kwallo a raga dole sai Chelsea ta zira kwallaye biyu kafin ta tsallake.

Jose Mourinho yace samun nasarar doke Atletico yanzu shi ne babban kalubalensa, akan haka kuma zai ajiye ‘manyan zaratan ‘Yan wasan shi a babbar karawar da zai yi da Liverpool a Premier League a ranar Lahadi. Wanda hakan ke tabbatar da Mourinho ya hakura da kofin Premier

A yau Laraba ne kuma za’a fafata tsakanin Real Madrid da Bayern Munich mai rike da kofin gasar. Har yanzu kuma dai ana hasashen ko Cristiano Ronaldo ba da shi za’a yi karawar ba saboda bai ida murmujewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.