Kwallon kafa

UEFA Zata dauki mataki kan kudaden da kungiyoyi ke kashewa

Shugaban hukumar kwallon kafa ta UEFA, Michel Platini
Shugaban hukumar kwallon kafa ta UEFA, Michel Platini

Shugaban hukumar kwallon kafa ta UEFA, Michel Platini, ya ce za a dauki tsauraran matakai kan duk wata kungiyar kwallon kafa da aka samu da laifin wuce adadin kudaden da doka ta tanada su kashe.

Talla

Ko da yake Platini ya ce tsauraran matakan ba za su hada da haramtawa wata kungiya buga gasar zakarun nahiyar Turai ba.

A farkon makon nan ne, wasu kafofin yada labarai suka ruwaito cewa kungiyar Manchester City ta Ingila da kuma Paris Saint Germain ta Faransa sun kashe kudade fiye da adadin da aka shata.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.