Yaya Toure yana nazarin ficewa City
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga Birtaniya na cewa akwai yiyuwar Yaya Toure na Cote d’Ivoire zai fice daga Manchester City saboda baya jin dadi a kungiyar. Wakilinsa yace Toure zai fice kungiyar ne saboda yadda shugabannin Manchester City ba su darajja shi.
Kuma Yaya toure wanda ya zirara wa Manchester city kwallaye 20 a raga a bana ya gasgata ikirarin na wakilinsa a wani sako da ya aika a Twitter.
Toure yace ya cancanci abin kulawa ga shugabaannin kungiyar saboda irin rawar da ya ke takawa a Manchester City amma cikinsu babu wanda ya aiko masa da sakon fatar alheri a lokacin da ya ke bikin ranar haihuwarsa.
Yaya Toure dai yanzu yace idan an kammala gasar cin kofin Duniya a Brazil zai bayyana makomar shi a Manchester City.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu