Wasanni

FIFA za ta fitar da sakamakon binciken zargin rashawa a ran 9 ga watan yuni

Alamar hukumar FIFA
Alamar hukumar FIFA SEBASTIEN BOZON / AFP

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta ce a ranar 9 ga wannan wata na yuni ne za ta kammala aikin bincike a game da zargin cewa an tafka gagarumin kuskure wajen bai wa kasar Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a 2018 da kuma irin wannan dama da aka bai wa kasar Qatar wato 2022.

Talla

Biyu daga cikin masu aikin binciken wato Micheal J. Garcia da kuma Cornel Borbely, sun shaida wa wani taron manema labarai cewa bayan kammala binciken a ranar 9 ga wannan wata, za su mika sakamakon aikinsu ne ga hukumar ta FIFA a cikin makonni 6 da za su biyo baya.

Yanzu haka dai mahawara ta kaure tsakanin masu shawar kwallon kafa, musamman a game da zargin bayar da rashawa ko kuma toshiyar baki ga masu jefa kuri’a da ake yi wa kasar Qatar.

A ranar litinin da ta gabata, kasar Australia daya daga cikin kasashen da Qatar ta kayar a neman wannan matsayi, ta sanar da kaddamar da wani yunkuri domin ganin cewa an kwace gasar daga hannun Qatar domin bai wa kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.