Wasanni

Frank Lampard zai bar Chelsea bayan share shekaru 13 a wannan kulob

Frank Lampard
Frank Lampard

Shahrarren dan wasan Chelsea wato Frank Lampard ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga wannan kulob da ya share shekaru 13 a cikinsa.

Talla

Shi dai Lampard, ya kulla kwantaraginsa na farko da Chelsea ne a shekara ta 2001, kuma a cikin wadannan shekaru ya buga wasanni har sau 649, yayin da ya taimaka wa Chelsea har ta dauki kofuna 11 a matakai daban daban, da suka hada da kofin gasar premier sau uku da kuma kofin zakarun nahiyar Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.