Brazil 2014: Gasar Cin Kofin Duniya

'Yan kasar Brazil a filin wasa na Maracanã, a Rio de Janeiro.
Chanzawa ranar: 19/06/2014 - 14:14

Wannan ne karo na 20 da za’a gudanar da Gasar cin Kofin Duniya a Brazil inda za’a kwashe tsawon wata guda daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli. Karo na biyu ke nan da Brazil ke daukar nauyin gasar, tun a karon farko a 1950. Kasashe 32 ne zasu fafata a gasar har da Brazil da ke karbar bakuncin gasar, kuma za’a buga wasanni 64 a biranen Brazil 12.