Tennis

Nadal ya doke Ferrer a Roland Garros

Dan wasan Tennis Rafael Nadal
Dan wasan Tennis Rafael Nadal RFI / Pierre René-Worms

Rafael Nadal ya doke dan uwansa David Ferrer na Spain a zagayen kwata Fainal a gasar Tennis ta Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa. Nadal da ke harin lashe kofin gasar karo na 9 ya tsallake ne zagayen dab da na karshe a gasar inda zai hadu da Andy Murray na Birtaniya wanda shi ma ya doke Gael Monfils.

Talla

A gobe Juma’a ne kuma Navak Djokovic zai kara da dan kasar Latvia Ernests Gilbis a zagayen dab da na karshe.

Bangaren Mata

Andrea Petkovic ta Jamus, ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe bayan ta doke Sara Errani ta Italiya, yanzu kuma zata kara ne da Simona Halep.

Petkovic dai ita ce yanzu ‘Yar kasar Jamus ta farko da ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe tun 1999 zamanin Steffi Graf jarumar Tennis ta Jamus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.