Kwallon Kafa

Zuwan Diego Costa a Chelsea

Dan wasan Atletico Madrid Diego Costa.
Dan wasan Atletico Madrid Diego Costa. REUTERS/Sergio Perez

Jaridun Birtaniya sun ruwaito cewa Chelsea ta kammala diba lafiyar Diego Costa na Atletico Madrid kafin kammala cinikinsa, kamar yadda jaridun Birtaniya suka ruwaito. Sai dai kuma Rahotanni da suka fito daga Spain sun ce Atletico Madrid ta karyata ikirarin akan Chelsea na dab da kammala cinikin dan wasan.

Talla

Jaridar Guardian tace Chelsea ta diba lafiyar dan wasan tare da yin hasashen zai kai kudi Fam miliyan 32.

Wasu Jaridun Spain sun ruwaito shugaban Atletico Madrid yana cewa ko Chelsea zata mallaki dan wasan sai ta biya adadin kudin da ke kan wuya dan wasan da kuma kudaden da suke bukata da suka kai euro Miliyan 40.

A bana dai Costa ya jefa wa Atletico kwallaye 36 a raga tare da taimakawa kungiyar lashe kofin La liga a karon farko tsawon shekaru 18.

Kwallayen da kuma dan wasan ya jefa a raga a bana duka sun zarce adadin kwallayen da maciya raga a Chelsea suka zirara, wato Torres da Eto’o da kuma Demba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.