Kwallon Kafa

Mourinho yana son Fabregas a Chelsea

Cesc Fabregas dan wasan Barcelona
Cesc Fabregas dan wasan Barcelona REUTERS/Gustau Nacarino

Jose Mourinho na Chelsea ya tabbatar da bukatar shi akan Cesc Fabregas na Barcelona, wanda tsohon dan wasan Arsenal ne da ke adawa da Chelsea a Ingila. Mourinho dai yace ya lura Fabregas yana son barin Barcelona, kuma yana son ne ya koma Ingila don haka ya ke da yakinin mallakar dan wasan.

Talla

Mourinho wanda ke yi wa Yahoo fashin baki a gasar cin kofin duniya da za’a gudanar a Brazil, yace yana nazari akan dan wasan.

A 2011 ne Fabregas ya baro Arsenal zuwa Barcelona kuma ya lashe kofuna biyar a Barcelona, kungiyar da ta reni shi yana karami.

Gerard Pique ya kwarmata cewa Barcelona zata sayar da Fabregas akan kudi euro Miliyan 33, a lokacin da ya ke zantawa da kocin Spain Vicente del Bosque.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.