Roland Garros

Sharapova da Halep a karawar Karshe

Maria Sharapova a gasar Roland Garros
Maria Sharapova a gasar Roland Garros Reuters/Gonzalo Fuentes

Maria Sharapova da Simona Halep sune jaruman Tennis din da zasu yi karawar karshe a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa. Wannan ne karo na uku da Sharapova ke tsallakewa zuwa zagayen karshe a jere da jere bayan ta doke Eugenie Bouchard ta Canada 4 da 6, 7 da 5, 6 da 2.

Talla

Simona Halep kuma ta doke Andrea Petkovic, ne ci 6 da 2, 7da 6 (7 da 4), a fafatawar dab da na karshe da ya basu damar tsallakewa zuwa karawar karshe a gobe Assabar.

Yau Juma’a dai aka shiga kwanaki na 13 a gasar kuma, akwai Jaruman Tennis na duniya da zasu fafata a bangaren maza.

Rafael Nadal wanda ke harin lashe kofin gasar a karo na 9 zai kara ne da Andy Murray na Birtaniya, yayin da kuma Novak Djokovic zai fafata da Ernests Gulbis.

Ana gudanar da gasar ne a fili mai kasa, kuma Nadal gwani ne domin sau takwas yana lashe kofin Roland Garros, Andy Murray kuma wanda ya lashe Wimbledon, wannan ne karon farko da ya ke kokarin lashe kofin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.