Kwallon Kafa

Amurka ta doke Najeriya

Fafatawa tsakanin Najeriya da Amurka
Fafatawa tsakanin Najeriya da Amurka Reuters

Kasar Amurka ta doke Najeriya ci 2 da 1 a ranar Assabar a wasan sada zumunci da kasashen biyu suka fafata domin shirye shiryen shiga gasar cin kofin duniya a Brazil.Dan wasan Sunderland Jozy Altidore shi ne ya jefa wa Amurka dukkanin kwallayen a ragar Najeriya, yayin da kuma Victor Moses ya samu nasar jefa wa Najeriya kwallo a bugun Fanalti saura minti hudu a kammala wasa.

Talla

Wannan ne karo na biyu da kasashen biyu suke haduwa tun haduwarsu a 1995 da Amurka ta doke Najeriya ci 3-2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.