Kwallon Kafa

Maradona ya soki FIFA

Diego Maradona na Argentina
Diego Maradona na Argentina Reuters

Tsohon fitattacen dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona ya soki  FIFA game da badakalar cin hanci da ke tattare da hukumar mai kula da sha’annin kwallon kafa a duniya. Maradona ya nemi a dauki mataki akan batun Qatar da ake zargin an karbi cin hanci kafin a ba kasar nauyin daukar gasar cin kofin duniya a 2022.

Talla

Maradona ya shaidawa Jaridar Al Itthad ta Abu Dhabi cewa cin hanci ya yi katutu a hukumar FIFA, tare da kira a dauki mataki akai.

Yanzu haka dai Kasar Qatar da Jami’an hukumar FIFA suna fuskantar matsin lamba akan karbar cin hanci kafin a ba kasar damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekarar ta 2022.

Jaridar Sunday Times a Birtaniya ta yi kwarmaton cewa ta samu sakwanni masu dimbin yawa da wasu takardu da ke nuna tsohon shugaban kwallon yankin Asiya Bin Hammam ya biya kudade sama da Miliyan 5 domin ganin Qatar ta samu nasara.

A ranar Litinin ne dai ake sa ran FIFA zata bayyana sakamakon bincikenta game da al’amarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.