Tennis

Sharapova ta lashe Roland Garros

Maria Sharapova rike da kofin  gasar Roland Garros da ta lashe karo na biyu
Maria Sharapova rike da kofin gasar Roland Garros da ta lashe karo na biyu REUTERS/Vincent Kessler

Maria Sharapova Jarumar Tennis a Rasha ta lashe kofin Roland Garros karo na biyu a cikin shekaru uku bayan ta doke ‘yar wasan Romania Simona Halep a karawar karshe da aka kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa. Wannan shi ne kofi na biyar da Sharapova ta lashe na manyan gasannin Tennis na duniya.

Talla

A shekarar 2012 Sharapova ita ce ta lashe kofin gasar a Faransa yayin da kuma a bara ta sha kashi a karawar karshe a hannun Serena Williams.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.