Kwallon kafa

Batun Qatar na da nasaba da wariyar launin fata- Blatter

Sheikh Mohammed bin Hamad bin Khalifa Al Thani, de la famille royale du Qatar, et le président de la Fédération internationale de football, Josep Blatter, en novembre 2013.
Sheikh Mohammed bin Hamad bin Khalifa Al Thani, de la famille royale du Qatar, et le président de la Fédération internationale de football, Josep Blatter, en novembre 2013. AFP PHOTO / AL-WATAN DOHA / KARIM JAAFAR

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter ya mayar da martani kan wadanda ke zargin hukumar da karbar cin hanci wajen bayar da daukar nauyin gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022, inda ya ce mutanen dake wannan zargi, so kawai suke su wargaza hukumar ta FIFA. 

Talla

Dan shekaru 78, Blatter ya yi wadannan kalamai ne yayin wata ganawa da ya yi da hukumomin kwallon kafa na nahiyar Asiya da Afrika, yayin da ake shirin bude taron wakilan hukumar ta FIFA a karo 64 a yau Talata.

Ya kuma kara da cewa zargin da ake yi kan badakalar ta Qatar na da nasaba da wariyar launin fata idan aka kalli lamarin ta wata fuska.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.