FIFA

Blatter zai yi tazarce

Joseph Blatter Shugaban hukumar kwallon duniya FIFA
Joseph Blatter Shugaban hukumar kwallon duniya FIFA REUTERS/Paulo Whitaker

Shugaban hukumar FIFA da ke kula kwallon kafa a Duniya, Sepp Blatter, ya bayyana kudirinsa na sake neman wa’adin shugabancin hukumar, yana mai yin watsi da kiranye kiranyen jami’an kwallon Turai da suka bukaci ya jingine kudirin saboda badakalar cin hanci da ya dabaibaye hukumar.

Talla

Blatter dai ya fadi kudirinsa na sake tsayawa takara ne a birnin Sao Poulo na Brazil a jiya Laraba jajibirin bude wasannin gasar cin kofin duniya.

A badi ne wa’adin shugabancin Blatter zai kawo karshe, amma shugaban na kwallon duniya yace bai kammala cim ma muradin shi ba.

Blatter ya kwashe tsawon shekaru kusan 14 yana jagorantar hukumar FIFA, amma batun badakalar ba Qatar nauyin karbar bakuncin gasar Cin kofin duniya a 2022 yana neman zama barazana ga Blatter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.