Brazil

Gasar cin kofin duniya a Brazil

Wani Yaro a Hong Kong yankin tsibirin Cheung Chau yana wasa da wani kofin Jabu na gasar cin kofin duniya da za'a gudanar a Brazil
Wani Yaro a Hong Kong yankin tsibirin Cheung Chau yana wasa da wani kofin Jabu na gasar cin kofin duniya da za'a gudanar a Brazil Reuters/路透社

A yau Alhamis za’a fara buga wasannin gasar cin kofin duniya a Brazil, wasannin da ake fatar zasu hada kan mutanen kasar saboda zanga-zangar adawa da kudaden da aka kashe domin karbar bakuncin gasar.

Talla

Akwai dai yanzu matakan tsaro da gwamnatin Brazil ta dauka domin ganin an gudanar da wasannin cikin kwanciyar hankali, bayan shafe kwanaki ana zanga-zanga a kasar.

Kasar Brazil ce dai zata fara kece raini da Croatia a birnin Soa Poulo a yau Alhamis.
Wannan ne karo na 20 da za’a gudanar da Gasar a Brazil inda za’a kwashe tsawon wata guda daga yau ranar 12 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.

Karo na biyu ke nan da Brazil ke daukar nauyin gasar, tun a karon farko a 1950.
Kasashe daga nahiyoyin duniya 32 ne za su fafata a gasar har da Brazil da ke karbar bakuncin gasar, kuma za’a buga wasanni 64 a biranen Brazil 12.

Mai horar da ‘yan wasan Brazil Luiz Felipe Scolari ya yi kira ga ‘yan kasar su kai zuciya nesa domin fitowa su marawa kasar baya wajen ganin ta cim ma nasarar lashe kofin gasar
Gasar cin kofin duniya dai fage ne na bajakolin ‘yan wasa musamman matasa wadanda zasu yi kokarin nuna bajinta domin samun manyan kungiyoyi a Turai.

Gasar kuma a bana ta kunshi zaratan ‘Yan kwallon duniya guda biyu Lionel Messi na Argentina da Cristiano Ronaldo na Portugal wadanda zasu yi farautar lashe kofin gasar domin neman ci gaba da matsayinsu na manyan ‘Yan wasan duniya.

Sai a gobe Juma’a ne kuma Kamaru daga Nahiyar Afrika zata fara karawa da Mexico a fafatawar rukuninsu na A, kuma Samuel Eto’o da ke jagorantar kamaru yace a bana za su taka rawar gani lura da matakin farko da ake yin waje da su a gasannin da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.