Brazil 2014

Spain zata lashe kofin duniya a Brazil-Hasashe

Tawagar 'Yan wasan Spain
Tawagar 'Yan wasan Spain fifa.com

Wata cibiyar da ke sa ido ga sha’annin kwallon kafa a kasar Switzerland, ta yi fashin baki akan cewa kasar Spain ce zata lashe kofin gasar cin kofin duniya, saboda zubin zaratan ‘Yan wasan da kasar ta tara. Kuma a cikin sharhin na cibiyar tace Spain da Brazil ne za su kai ga zagayen karshe, amma Spain ce zata lashe kofin.

Talla

Cibiyar CIES Football Observatory tace ta yi nazari akan dukkanin kasashen da zasu haska guda 32, kuma sakamakon binciken ya nuna cewa Spain ce zata doke Brazil a wasan karshe, sai Argentina a matsayi na uku, Faransa kuma a matsayi na hudu.

A cikin hasashen, cibiyar da ke nazarin kwallon kafa tace Faransa ce zata yi waje da Najeriya a zagaye na biyu, kamar yadda Portugal zata kori Rasha.

Kasar Spain dai zata yi kokarin kare kofin gasar ne da ta lashe a Afrika ta kudu, wanda a tarihin gasar kuma babu wata kasa da ta iya kare kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.